fidelitybank

Gwamnati ta bayyana sunan masu daukar nauyin ta’addanci – Ndume

Date:

Shugaban kwamitin majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ali Ndume, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayen wadanda ke bayar da kudade a kan ta’addanci a kasar nan tare da kama su.

Da ya ke magana a wata hira da a ka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV’s Paradigm, Ndume, ya ce, gwamnatin tarayya ta tuhume shi da daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Laifin nasa, in ji shi, shi ne saboda, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bi diddigin waya tare da gano kiran da kakakin ‘yan ta’addan ya yi.

Yayin da ya ke lura da cewa an kama shi, dan majalisar ya soki hukumomin tsaro da rashin gudanar da bincike mai kyau kafin su yi masa ba asi.

“Idan akwai hujjojin da ke nuna cewa wani ya na tallafa wa Boko Haram, akwai kwararan hujjoji bayan gudanar da bincikenku, me ya sa ba za ku fadawa ‘yan Najeriya ba? Me ya sa ba za ku gurfanar da su a gaban kuliya ba?” Ya tambaya.

“Saboda su na bibiyar wayata sai su ka ce mai magana da yawun Boko Haram ya kira ni, sai suka je su ka kama ni. Ba su ma tambaye ni ba, ba su yi wani aikin hankali ba. Shugaban majalisar dattawa ya kira ni ya ce SSS na da wasu tambayoyi.”

A cewar dan majalisar, ya kai rahoto a ofishin DSS ya na tunanin za a ba shi damar amfani da bayanan da za su taimaka wajen yakin ta’addanci.

Ya tuna cewa mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Marilyn Ogar, ta yi wa manema labarai karin haske inda ake zarginsa da daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Sanatan ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sake gina yankin Arewa maso gabas da rikicin tada kayar baya ya daidaita sama da shekaru goma.

A wani bangare na yunkurin sake ginawa, Ndume ya bukaci hukumomin kasar da su tsugunar da wadanda ta’addancin ya rutsa da su, da sake gina wuraren da suka lalata, tare da bayyana masu tayar da kayar baya wadanda bisa radin kansu su ke mika wuya ga hukumomin soja.

Baya ga tada kayar baya, ya kuma mayar da martani kan kin amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na kin amincewa da kudirin gyaran dokar zabe.

Ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka ya zo wa majalisar da kaduwa duk da kokarin da ‘yan majalisar su ka yi wajen tsara kudirin.

 

 

punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

‘Yan sa-kai biyu ne suka mutu a harin da muka kai Zamfara – Sojoji

Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai...

Dakarun sojin ruwa a Najeriya sun yi kaɗan wajen tsaron ƙasa – Emmanuel Ogalla

Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa...

Juma’a da Litinin ranakun hutun Sallar Layya – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma'a da Liitnin masu...

Gwamnatin Neja zai haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man fetur

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya nemi aikin haɗin...

Tchiani ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da Nijar

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya...

An ceto yara 12 da aka yi safararsu a jihar Abia

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami'anta sun samu...

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...
X whatsapp