fidelitybank

Gwamnati na kashe Niara biliyan 1 wajen biyan ma’aikatan FAAN dun shekara – Keyamo

Date:

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Jiragen Sama Festus Keyamo, ya ce Gwamnatin Najeriya na kashe Naira Biliyan 1 wajen biyan tallafin kudin alawus na Duty Tour Allowance (DTA) da tikitin jirgin sama ga Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Tarayyar Najeriya, FAAN, jami’an da ke kai da kawowa daga Abuja zuwa Legas, duk shekara.

Keyamo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wata sanarwa da ya fitar da ke fayyace kalamansa na ā€˜DTA ma’aikatan FAAN N500 a gidan Talabijin na Channels.

A cewarsa, a shekarar 2023 ma’aikatan FAAN sun kashe N493,678,620.37 akan DTA da kuma N451,058,950.09 na tikitin jirgi.

ā€œLokacin da na yi hira da gidan talabijin na Channels a jiya, ba a yi mini bayani ba game da kudaden da FAAN ta kashe a shekarar da ta gabata a kan DTA (Duty Tour Allowance) ga manyan jami’an da ke kai da komowa daga Legas zuwa Abuja kusan kullum.

ā€œKudin ya kai N493,678,620.37. Baya ga tikitin jirgin da na ambata ya kai N451,058,950.09.

ā€œDon haka, a dunkule, saboda dagewar da aka yi na nada Abuja a matsayin hedikwatar FAAN (lokacin da babu ofisoshi a Abuja da zai dauki dukkan manyan jami’an FAAN), FAAN ta kashe kusan Naira biliyan daya a shekara guda,ā€ inji shi.

DAILY POST ta rahoto cewa Ministan ya dage kan ci gaba da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na mayar da hedikwatar FAAN zuwa Legas duk da adawar da wasu bangarorin suka yi.

Ku tuna cewa a ranar 19 ga watan Janairu, 2023, Keyamo ya sanar da sauya shelkwatar FAAN daga Abuja zuwa Legas.

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp