fidelitybank

Gwamnati ki kare ‘yan Jarida a zaben 2023 – CJID

Date:

Cibiyar kirkire-kirkire da ci gaban aikin jarida, CJID, ta shawarci gwamnatin Najeriya da ta mutunta tare da kare ‘yancin ‘yan jarida, ta yadda ‘yan jarida za su yi aiki cikin walwala ba tare da cin zarafi ba kafin, lokacin da kuma bayan zaben 2023.

Cibiyar ta kara da cewa ya kamata gwamnati ta tabbatar da cewa ba a cin zarafin ‘yan jarida ko kuma tsoratar da ‘yan jarida a yayin da suke yada labaran zabe kamar yadda aka yi a zabukan da suka gabata.

Shugaban harkokin siyasa a babbar hukumar Kanada a Najeriya, Andy Web ne ya yi wannan kiran yayin jawabinsa a wani taron manema labarai mai taken “Zaben 2023: Tsaro, Kafafen Yada Labarai da Safety,” a karshen mako.

Karanta Wannan: Ƙungiyar Kiristoci ta jinjina wa Buhari a kan zaɓen 2023

Babban kwamishinan yayin da yake lura da cewa wasu jami’an gwamnatin Najeriya na amfani da son zuciya wajen magance rikice-rikicen kafafen yada labarai da hukumomin kasar, yana mai ba da tabbacin gwamnatin Canada na goyon bayan ‘yancin yada labarai a Najeriya a kowane lokaci.

Ya ce: “Muna kira ga gwamnati da ta mutunta ‘yancin yada labarai domin ‘yan jarida su yi aiki cikin walwala ba tare da an ci zarafinsu ba.

“Taron shine don tunawa da ranar duniya don kawo karshen rashin hukunta masu aikata laifukan da ake yi wa ‘yan jarida kuma martani ne ga ci gaba da barazana ga tsaron lafiyar ‘yan jarida, da kuma fargabar abin da ka iya tasowa bayan zabukan 2023 a kasar.”

Babban mai jawabi, Farfesa Umaru Pate, mataimakin shugaban jami’ar tarayya Kashere, ya bayyana cewa zabuka a Najeriya na da matukar hadari da tashin hankali, inda ya yi nadamar cewa ‘yan jarida ne suka fi fuskantar matsalar.

Ya kara da cewa, a zaben 2019 an ci zarafin wasu ‘yan jarida tare da tsare wasu gidajen yanar gizo guda 20, tare da tsoratarwa, ba tare da wani yunkurin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya ba.

“Wannan zai sa ƙungiyoyin watsa labarai su kasance masu yin katsalandan da kansu wanda ke raunana aikin jarida na bincike,” in ji shi.

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp