fidelitybank

Gwamnati da ASUU su warware matasalar yajin aiki – Sanusi

Date:

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Lamido Sanusi, ya bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su warware rikicin da ya dabaibaye su a kan yajin aiki.

Sanusi ya yi wannan kiran ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a birnin New York na kasar Amurka, a ci gaba da taron koli na sauya fasalin ilimi na kwanaki uku.

Sanusi ya ce za a iya magance yajin aikin ASUU ta hanyar tattaunawa, yana mai cewa akwai bukatar kungiyar ta san cewa tsawon lokacin da ta aka yi ba a zuwa makaranta, daliban ne za su sha wahala.

“Ya kamata gwamnati ta gane cewa malamai mutane ne; muna cikin kasar da ake fama da hauhawar farashi kuma albashi ba ya kai malamai ko’ina kuma koyarwa sana’a ce da ya kamata a ba ta daraja daga mafi karanci zuwa babba.

“Ma’aikatanmu na ilimi ma’aikatan kiwon lafiya ne ma, abin da ba mu sani ba shi ne mun yi asarar malamai da yawa, yawancin mutanen da ke fita kasashen waje don yin PhD ba sa dawowa.

“Likitoci da yawa da ke aiki a Najeriya sun fita kasashen waje,” in ji shi.

Tsohon shugaban babban bankin na CBN, wanda shine Sarkin Kano na 14, ya ce zubar da kwakwalwa ya yi illa ga tattalin arziki.

“Rikici ne saboda muna bukatar likitoci a Najeriya, muna bukatar malamai a Najeriya saboda mun saka jari sosai wajen horar da su.

“Dukan bangarorin biyu (ASUU da Gwamnatin Tarayya) suna da ruwa da tsaki wajen zama a yi tattaunawa, yin sulhu, na yi imanin za a iya warware shi cikin gaskiya,” inji shi.

Sanusi ya kuma bukaci gwamnati da ta saka hannun jari a fannin ilimi domin karfafa gwiwar malamai su kasance masu iya kokarinsu, ya kara da cewa a lokutan baya malamai sun kasance suna mutunta daraja a cikin al’umma a baya, ya kara da cewa “amma yanzu mutane sun raina darajar ilimi.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp