fidelitybank

Gwamnan Yobe ya janye dokar hawa Babur a jihar bayan shekaru 10

Date:

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya dage dokar hana amfani da babura a yankunan Arewaci da Kudancin jihar.

Hakan dai ya biyo bayan komawar al’amura a galibin yankunan tare da komawar hukumomin farar hula.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara fadar Sarkin Nguru, domin jajanta wa jama’a kan aukuwar gobara da ta lalata kadarori na miliyoyin Naira a kasuwar Nguru.

Buni ya ce”A yanzu mazauna garin sun samu damar hawan Babura, domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

“Da wannan ne mu ke gudanar da wani bangare na yakin neman zabe, domin dawo da zaman lafiya a jihar da kuma ba da damar amfani da Babura, domin bukatun jama’a,” inji shi.

Kananan hukumomi 10 da aka amince su yi amfani da baburan sun hada da Fika, Nangere, Fune, Potiskum, Jakusko, Bade, Nguru, Karasuwa, Yusufari da Machina.

Sai dai matakin ya ta’allaka ne da wasu sharudda takwas da masu tuka mota suka cika, daya daga cikinsu shi ne cewa dole ne su rika gudanar da aiki daga karfe shida na safe zuwa karfe 6 na yamma a kowace rana kuma kada a yi amfani da su wajen tallan kabu-kabu (Achaba). Mahayi daya ne kawai za a yarda ba tare da wani mutum a kan babur ba.

Ya ce”Dole ne a samar da ingantaccen rajista, lasisi da takaddun duk babura da masu keke a cikin kananan hukumomin da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Yobe (YROTA) ke aiwatarwa”. A cewar Buni.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar Yobe ta haramta amfani da babura a daidai lokacin da rikicin Boko Haram ya barke a cikin shekaru 12 da suka gabata.

nnnhausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp