Gwamnan jihar River Siminalayi Fubara, ya karrama golan Najeriya, Stanley Nwabali sakamakon bajintar da ya nuna gasar kofin ƙasashe Afirka ta Afcon da aka kammala makon da ya gabata.
A bikin da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, gwamna Fubara ya bai wa golan – wanda ɗan asalin jihar ne – kyautar zunzurutun kuɗi naira miliyan 20.
Haka kuma gwamnan ya karrama shi da lambar yabo ta DSSRS, lambar yabo ta biyu mafi daraja da ake bai wa wadanda suka yi bajinta a fannoninsu, da manyan ‘yan siyasa a jihar.
Gwamnan ya kuma bai wa tawagar Super Eagles da ta samu wakilcin kocin tawagar Jose Peseiro da Finidi George kyautar naira miliyan 30, sakamakon bajintar da ƙungiyar na nuna a gasar.
Najeriya dai ta ƙare gasar a matsayi na biyu, bayan da ta sha kashi a hannun Ivory Coast mai masaukin baƙi da ci 2-1 a wasan ƙarshe.


