fidelitybank

Gwamnan Kaduna ya dawo da rawanin Sarkin da El-Rufa’i ya tsige

Date:

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya mayar wa Jonathan Paragua Zamuna rawaninsa na Sarkin Piriga.

 

Gwamnan ya ce ya mayar wa sarkin rawaninsa ne bayan kotun ma’aikata ta jihar ta yanke hukuncin soke cire masa rawanin.

 

A zamanin tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufai ne aka tuɓe rawanin sarkin, amma daga bisani sarkin ya kai ƙara kotu, inda a ranar 14 ga Yunin 2024, kotu ta soke cire sarkin, kamar yadda Channels ta ruwaito.

 

Uba Sani ya taya sarkin murnar komawa kujerarsa, sannan ya yi kira a gare shi da ya yi adalci ga kowa ba tare da nuna bambancin addini da ƙabila.

 

“Gwamnatinmu tana bin doka da oda. Wannan ne ya sa ba mu ɓata lokaci ba wajen ɗabbaƙa hukuncin kotun ma’aikata na mayar wa Sarkin Piriga rawaninsa,” in ji shi.

 

A nasa ɓangare, Sarkin Piriga, ya yi godiya ga gwamnan bisa mayar masa da rawani, inda ya ƙara da cewa akwai ƙabilu 12, kuma suna zama lafiya tare da juna.

punch news paper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...
X whatsapp