An hana mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, shiga ofishinsa da ke gidan gwamnati a Benin babban birnin jihar.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, Shaibu ya isa gidan gwamnatin ne da safiyar yau Litinin, inda ya iske kofar shiga ofishin nasa a kulle.
Ya ce bai samu wata takarda daga ofishin gwamnan ba, da ke umurtar sa da sauya wurin aiki, wanda kuma ita ce ya kamata ta zama hanyar ba shi umarnin barin ofishinsa da ke gidan gwamnati.
“Har yanzu ban samu wata sanarwa ba a hukumance da aka umarce ni na canza ofis.
“Ma’aikatan ofis dina ne kawai suka samu saƙon, ba ni ba.”
“A yanzu haka da nake magana da ku, ina tsaye a bakin kofa,” in ji shi yayin da yake tattaunawa da wani wanda ba a san ko wane ne ba.
A makon da ya gabata, an aika da wata wasiƙa daga ofishin shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar, wadda ke ɗauke da saƙon umurni ga mataimakin gwamna, Philip Shu’aibu kan cewa an mayar da ofishinsa zuwa gini mai lamba 7, Dennis Osadebey Avenue, GRA, Benin City.


