fidelitybank

Gwamna mai jiran gado Soludo ya nada kwamitin rantsar da shi

Date:

Zababben gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin mika mulki mai wakilai 80 da za su taimaka wajen rantsar da shi a ranar 17 ga Maris, 2022.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, jiya, ta hannun mai taimaka wa Soludo kan harkokin yada labarai, Joe Anatume, jerin sun kunshi mambobi 80, tare da fitattun ‘yan Najeriya, wadanda za su taka rawa daban-daban.

Ya ce, kwamitin zai tuntubi tawagar da gwamnatin jihar Anambra ta kafa, domin tabbatar da karbar mulki daga hannun gwamnatin Willie Obiano zuwa gwamnatin Soludo daga ranar 17 ga Maris, 2022.

Sanarwar ta tabbatar da cewa, tsohuwar ministar ilimi, Dr. Oby Ezekwesili, ita ce shugabar kwamitin, yayin da Farfesa Benedict Oramah, Farfesa Pat Utomi da Osita Chidoka za su taka muhimmiyar rawa wajen shirin mika mulki.

Sauran mambobin sun hada da: Uche Okafor, Farfesa Chidi Odinkalu, Steve Nworga, Ben Nwankwo, Charles Odedo, Tony Ifeanya, Ferdinand Agu, Farfesa Osita Ogbu, Chikwe Udensi, Greg Ibe da Alex Otti, da dai sauransu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, za a sanar da sharuddan kwamitin, da kuma yadda za a gudanar da shi a yayin kaddamar da taron farko da kuma zaman taron farko da aka shirya gudanarwa tsakanin 19 da 22 ga watan Janairu, 2022 a otal din Golden Tulip (Agulu Lake) da ke cikin Otal din Golden Tulip (Agulu Lake) jihar

Har ila yau, ya ce, a na sa ran mambobin za su isa ranar Laraba 19 ga watan Janairu, yayin da za a fara taron kaddamar da taron farko a ranar 20 ga watan Janairu.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar Æ´an Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaÉ“e shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka Æ´an Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation HaÉ—in-Kai sun ce sun kashe Æ´an...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aÆ™alla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...
X whatsapp