fidelitybank

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Date:

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gidanke da ke birnin Legas.

Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya kai ziyarar ne tare da ƴan’uwansa, babban yayaransa Adedeji Adeleke, da kuma ɗandan’uwansa, fitaccen mawaƙin nan David Adeleke da aka fi sani da Davido, gabanin bukukuwan babbar sallah.

Kodayake babu cikakken bayani kan abin da tattaunawar tasu ta ƙunsa, ganawar na zuwa ne kwanaki bayan Davido ya gana da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a wani abu da ake ganin tattaunawa ce tsakanin dangin Adeleke da fadar shugaban ƙasar.

A cikin watan da ya gabata ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta saka ranar 20 ga watan Yulin 2026 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun.

Ana ganin Gwamna Adeleke – wanda ɗan jam’iyyar PDP ne – zai tsaya takara a zaɓn domin neman wa’adin mulkinsa na biyu, bayan da aka zaɓe shi a karon farko a 2022.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp