Koriya ta Arewa ta ce, gwajin makamai masu linzamin da ta yi sau bakwai a baya-bayan nan na nufin atisayen nukiliya.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce Shugaba Kim Jong-Un ne ya sa ido wajen gwada su.
Kamfanin Dillancin Labarai na KCNA ya ce atisayen sojojin da aka yi cikin makonni biyun da suka gabata na nufin daƙile yaƙin ƙasar da kuma tunkarar makaman nukiliya.
A gwajin da ta yi a baya-bayan nan, Koriya ta Arewa ta harba makamai biyu masu cin gajeren zango da suka bi ta sararin samaniyar Japan.
Pyongyang ta bayyana gwajin da ta yi a matsayin kare kai kan abin da ta kira barazana daga Amurka.