fidelitybank

Gobara a gidan Yari: Fursunoni 36 sun mutu

Date:

A ƙalla mutum 36 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata, sakamaon wata gobara da ta tashi a gidan yarin Burundi.

Mataimakin shugaban ƙasar, Prosper Bazombanza ya shaida wa manema labarai cewa, gobarar ta tashi ne a wani gidan yari mai cunkoso a babban birnin ƙasar Gitega, inda a ƙalla mutum 69 suka jikkata.

Hotunan da suka yaɗu a intanet sun nuna yadda ginin gidan ke ci da wuta sannan da tarin gawarwaki, waɗanda aka ce na fursunoni ne.

“Wannan babban bala’i ne,” kamar yadda wani fursuna ya shaida wa BBC ta waya.

“Zan iya cewa kusan kashi 90 cikin 100 na ɗakunan kwana sun ƙone ƙurmus.”

Wani ɗan jarida a wajen gidan yarin ya shaida wa BBC cewa ma’aikatan jinya daga asibitin Gitega sun shiga gidan yarin don taimaka wa waɗanda lamarin ya rutsa da su, yana mai cewa suna kwashe mamatan da waɗanda suka jikkata.

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 4 na yammaci agogon ƙasar, wato ƙarfe 2 agogon GMT.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp