fidelitybank

Giya: Hisba ta gamu da tutsu yayin sumame

Date:

A daren ranar Talata ne wata hatsaniya ta kaure tsakanin jami’an hukumar Hisbah ta Kano da wasu matasa a wata mashayar Barasa da ke unguwar Sabon Gari a cikin garin Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar Hisbah, sun dira a wani wajen shaye-shaye mai suna, Ballat Hughes da ke Court Road a cikin unguwar Sabon Gari.

Hukumar Hisba ta sami rahoton yadda a ke ta’ammali da Giya a wajen, domin kwace Barasa da sauran kayan shaye-shaye.

Lamarin da ya fusata matasan da ke wajen har ta kai ga sun fara jifan ‘yan Hisbah tare da fasa kwalaben giya, wanda ya kai ga samun hatsaniya a wajen.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa bayan faruwar lamarin, ‘yan daba da wasu bata gari sun yi amfani da wannan damar inda suka sace wasu muhimman kayayyaki a wajen.

Wannan lamarin ne ya sanya, shugaban hukumar Hisba, Muhammad Harun Ibn Sina, ya magantu, ya ce”Mun samu rahoton faruwar cewa a na tara mata da matasa a na koya musu shan Giya da kwaya a wajen, hakan ne ya sa mu ka kai sumame wajen, amma mun sami nasarar taho da mai siyar da Giyar a wajen, bayan an jefe mu da duwatsu, har da raunata jam’ian mu, kuma za mu gurfanar da mai siyar da Giyar a gaban kotu, domin ta girbi abin da ta shuka”. Inji Ibn Sina.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp