fidelitybank

Girgizar kasa ta kashe mutane 26 ‘yan gida daya a Afghanista

Date:

Akalla mutum 26 ne aka tabbatar da mutuwar su a gida daya, sakamakon wata girgizar kasa mai karfin mataki 5.3 a kasar Afghanistan.

Mutanen sun gamu da ajalinsu ne bayan rufin gidansu ya rufta a kansu a yankin Qadis da ke Yammacin Lardin Badghis na kasar.

A cewar mai magana da yawun Lardin Badghis, Baz Mohammad Sarwary.“Matan aure biyar da kananan yara hudu na daga cikin mutum 26 da suka rasu a girgizar kasar,”

Ya ce, girgizar kasar ta kuma lalata wasu gidaje a gundumar Muqr da ke cikin Lardin, sai dai ba a kai ga samun alkaluman wadanda lamarin ya shafa a yankin ba tukuna.

Yankin Qadis dai na daga cikin yankunan da matsalar karancin ruwan sama ta fi yi wa illa a kasar Afhganistan, kuma ta yi ta fama da rashin kayan agaji daga kasashen duniya a tsawon shekara 20 da suka gabata.

Kasar Afghanistan dai na yawan fama da girgizar kasa, musamman a yankin da Tsaunin Hindu Kush yake, wanda ke kan iyakokin kasar da nahiyar Turai da kuma Asiya ta bangaren Indiya.

 

punch newspaper headlines today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp