Hukumomi sun ce wani gini na rukunin gidaje a barikin ‘yan sanda da ke jihar Oyo ya rufta kan mutane.
Babu bayanai kan adadin mutane da ginin ya danne a barikin na Sango dake Ibadan babban birnin jihar.
Mazauna barikin na lalubawa cikin baraguzai da zummar ceto wadanda suke da sauran rai.
A farkon wannan watan ma dai wani bene mai hawa 7 da ba a kammala ginawa ba ya rufta kan mutane a yankin Banana Island dake Legas a Najeriyar.
Hukumomi dai suka ce ba a yi amfani da ingantattun kayan aiki ba yayin ginin


