fidelitybank

Ganduje ya sanya sunan Bashir Tofa a jami’ar Wudil – KCSF

Date:

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula a jihar Kano (KCSF), sun buƙaci gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya sauya sunan jami’ar Kimiyya da Fasaha mallakin jihar da ke garin Wudil, zuwa sunan marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa.

A cikin wata sanarwa ta’aziyya da KCSF ta aike waGanduje, mai ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar, Kwamared Ibrahim Waya da Sakataren ta, Peter Hassan Tijjani.

A cikin sakon ta’aziyyar, wacce jami’in yaɗa labarai na KCSF ɗin Kwamared MK Adam Rano ya rabawa manema labarai a Kano, sun bayyana marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa a matsayin ɗan kishin ƙasa da ya taka muhimmiyar rawa wajen cigaban jihar Kano da ma Arewacin Najeriya bki daya.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, Alhaji Bashir Tofa, ya rasu a dai-dai lokacin da ya ke tsaka da bayar da gudunmawar sa wajen cigaban al’umma ta hanyar taimaka musu a kan abubuwan da su ka addabe su tare da da ganin an samu hadin kai tsakanin ƴan Najeriya.

Hakazalika KCSF ta ƙara da cewa mutuwar Bashir Tofa ta haifar da wani babban giɓi da zai wahalar cikewa a nan kusa, musamman idan a ka yi la’akari da dattaku da ayyukan alkhairi da ya ke yi a lokacin rayuwarsa.

Alhaji Bashir Othman Tofa ya na daga cikin dattijan da su ka yi ta fafutukar ganin Arewacin Najeriya ya fita daga matsalolin tsaron da ya fada a ciki.

Haka kuma tarihin siyasar Najeriya ba zai taba cika ba, ba tare da an ambato Alhaji Bashir Usman Tofa, musamman kan abin da ya faru a shekarar 1993 lokacin zaɓen shugaban kasa.

 

sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp