Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara, domin duba aikin katafariyar Kasuwa ta zamani mai dauke maasallacin Juma’a da kuma makarantar Islamiyya.
Tsohon dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, kuma babban Darakta a hukumar Gidaje ta kasa Rt. Hon. Abdulmumin Jibril Kofa ne ya gina, domin bunkasa harkar kasuwanci a yankinsa.
Gwamna ya yabawa Kofa bisa wannan katafaren aiki da ya yi, inda ya yi alkawarin halartar bikin budewa idan an kammala.
Yayin ziyarar, Gwamnan ya na tare da mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinoni da masu baiwa Gwamna shawara.