Manyan jam’iyyun adawa a kasar Gambia sun yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa wanda a ka ayyana Adama Barrow a matsayin wanda ya yi nasarar.
Babban mai kalubalantar zaben, Ousainou Darboe na jam’iyyar UDP, ta re da wasu ‘yan takara Biyu, sun fitar da sanarwar ta hadin gwiwa a kan kin amincewa da sakamakon.
Sanarwar ta ce, sun fuskanci jinkiri wajen sanar da sakamakon karshe a zaben, kuma sun yi ikirarin cewa wakilan jam’iyyun su ba su amince da sakamakon zaben ba.
A shekara Biyar kenan da shugaban kasar Gambia, Adama Barrow ya hau karagar mulk, wanda ya kawo karshen mulkin, Yahya Jammeh na fiye da shekara 20.