Kungiyar Flying Eagles za ta fara shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 na shekarar 2023 a cikin sabon mako a Abuja.
Zakarun Afirka sau bakwai sun tafi hutu bayan halartar gasar cin kofin Afrika na ‘yan kasa da shekaru 20 na 2023 a Masar.
Tawagar Ladan Bosso ta zo ta uku a gasar.
Kasashen yammacin Afirka za su gano abokan karawarsu a gasar cin kofin duniya a karshen wannan watan.
Ana sa ran hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta bayyana sabon mai karbar bakuncin gasar a duk shekara a wannan makon bayan an cire Indonesia.
Argentina ce kasa daya tilo, da ta gabatar da kudirin karbar bakuncin gasar.
Za a gudanar da gasar ne daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Yuni.