fidelitybank

Fastocin Orji Kalu na takarar shugaban kasa sun karade Bauchi

Date:

Hotunan tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu na takarar shugaban kasa sun karade jihar Bauchi.

Wata kungiyar goyon bayan siyasa ta Kalu domin neman ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 ta manna fastocin Sanata Orji Uzor Kalu a manyan tituna da bangwayen gidaje a jihar.

Lamarin dai na zuwa ne makonni kadan bayan da wasu matasan Arewa suka kai Kalu gaban wata babbar kotun jihar Bauchi inda suka bukaci kotun ta tilasta masa tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Mazauna babban birnin jihar Bauchi sun wayi gari da ganin fastocin Kalu a ko’ina tare da nuna goyon bayansu ga Kalu a mtsayin shugaban Najeriya a 2023, wanda ya kau da kai wanda zai iya hada kan kasar da kuma ceto kasar daga tarwatsewar da ke kusa.

An hango fastocin a fadar Sarkin Bauchi da kewaye, babbar kasuwa, Awalah, hukumar kashe gobara, titin Jos da wasu hanyoyi da gidaje da dama.

Wasu daga cikin Fastocin Kalu da suka karade Bauchi.

Kungiyar ta kira Kalu a matsayin mafi kyawu a takarar shugaban kasa a 2023, inda ta bukace shi da ya tsaya takara a jam’iyyar APC.

Jikin shatale-tale a jihar Bauchi manne da hotun Kalu.

Kungiyar ta bukaci jam’iyyar APC da ta fara shirin daukar Kalu a matsayin dan takara daya tilo a jam’iyyar, saboda kwarewarsa na gudanar da mulki da gogewarsa da kuma kira ga kasa wanda ta ce shi ne ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2023.

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp