fidelitybank

Farashin Gas din girki ya ragu a Najeriya – Gwamnati

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce ta na daukar matakan da su ka dace, domin ganin an kara rage farashin iskar Gas din da a ka fi sani da gas din girki.

Gwamnati ta bayyana hakan ne yayin da ta ke mayar da martani ga raguwar farashin iskar gas a kwanan baya.

Bincike ya nuna cewa farashin LPG kilogiram 12.5 na gasa ya ragu daga Naira 8,800 zuwa tsakanin N8400 zuwa N8200. A wasu shagunan farashin ya ragu zuwa tsakanin Naira 7,800 zuwa N8,000 a ranar Alhamis.

A watan Nuwamba, farashin gas tashi sama da kashi 240 tsakanin Janairu da Oktoba 2021.

farashin ya karu da kashi 240 a kan kilo 12.5, inda ya tashi daga Naira 3,000 zuwa Naira 10,200 a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2021.

Kimanin kashi 65 cikin 100 na LPG a na shigo da su Najeriya ne, yayin da abin da a ke nomawa a cikin gida ya kai kashi 35 cikin 100, domin haka farashin kayayyaki a kasuwannin duniya ya shafi farashin cikin gida.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adeshina ya ce farashin LPG na duniya ya yi tashin gwauron zabi a cikin watan Oktoban bara, amma ya ragu zuwa karshen shekarar 2021 zuwa watan Janairun 2022, wanda hakan kuma ya taimaka wajen faduwar farashin gas na LPG a fadin kasar nan.

vanguard newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...

Luiz Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool

Luis Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool...

NNPCL ya musanta sayar da matatar mai ta Fatakwal

Babban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya musanta...

Mun samu kuÉ—in gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Abia – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ce, ta samu duka kuÉ—in gudanar...

Sanatocin Arewa sun yi tir da kisan Zamfara

Ƙungiyar sanatocin Arewa, ta yi Allah wadai da kisan...

Tattalin arzikin Najeriya zai kara bunkasa a shekarar nan – IMF

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta...

Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguzomomi ta kasa, ta fara...

Birtaniya ta na tsantsanr goyon bayam Hamas ne kawai – Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, matakin da Birntaniy...

Birtaniya ta gindaya wa Isra’ila sharuÉ—a

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya shimfiÉ—a wa Isra'ila wasu...
X whatsapp