Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kashe wata dalibar jami’ar Jos mai suna, Jennifer Antony mai karatun matakin ajin level 300.
da wasu da ba a san ko su wanene ba, wadanda ake kyautata zaton masu tsafi ne a wani otel da ke Jos.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda , Ubah Gabriel Ogaba ya shaida wa manema labarai cewa, rundunar ta samu kiran gaggawa game da lamarin, kuma a halin yanzu ta na kokarin bankado wadanda su ka aikata laifin.
An ce marigayiya Jennifer ta bace tun ranar 30 ga Disamba, 2021, kuma an gano gawar ta a ranar 1 ga Janairu an kwakwale mata idanu. An ce an kashe ta ne a wani otal da ke kan hanyar Zariya a garin Jos.
A na zargin cewa wasu da a ke zargin ‘yan tsafi ne su ka aikata kisan, inda a ke zargin sun yi amfani da miyagun kwayoyi kafin su cire idanuwan ta.
Ogaba ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya gudanar da taro da duk masu gudanar da otal a jihar tare da bullo da sabbin dabarun gano laifukan da ke kewaye da su.