Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai yi jawabin kawo karshen ayyukan sojin kasarsa a yankin sahel
Dakarun Faransa sun shafe shekara takwas suna yakar ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi a yankin.
A watan Fabrairu ne dai Faransa ta bayyana aniyar janye sosojinta daga kasar Mali.
Kimanin dakarun Faransa 5,500 ne ke aikin yaki da masu ikirarin jihadi a yankin na Sahel.
A shekarar 2013 ne aka kaddamar da dakarun wadanda ake yi wa lakabi da ‘Operation Barkhane’ domin dakile yaduwar masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.