Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da cewa ta fara kwashe ‘yan ƙasar daga Sudan tare da sauran jami’anta na diflomasiyya, waɗanda rikicin da ke gudana a ƙasar tsakanin sojoji da mayaƙan RSF ya rutsa da su.
Sanarwar Faransan na zauwa ne sa’o’i kaɗan bayan da shugaban Amurka Joe Biden, ya sanar da shirin Amurka na kwashe jami’an diflomasiyyarta da ke Khartoum.
Tun bayan ɓarkewar rikici tsakanin sojoji da dakarun RSF a ƙasar a ranar 15 ga watan Afrilu ake ba da rahoton mutuwar ɗaruruwan mutane wasu dubbai da dama kuma suka jikkata, yayin da wasu ke ci gaba da tsere wa daga ƙasar. In ji BBC.


