Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da murabus din Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, gabanin zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC a jihar Bayelsa a wata mai zuwa.
A ranar Juma’a, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa na zamani, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Ministan albarkatun man fetur, kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa, H.E. Timipre Sylva, ya yi murabus daga mukaminsa don tsayawa takara a zaben gwamnan Bayelsa mai zuwa,” Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sanarwar ta yi karin haske kan rade-radin da ke tattare da murabus din Ministan.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta tsayar da ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, domin gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo.
Maris 27 tsakanin Afrilu 17, 2023, an tsara ranakun da za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa.