fidelitybank

Everton ta naɗa Lampard a matsayin sabon Koci

Date:

Kungiyar Everton ta naɗa tsohon ɗan wasan Ingila kuma tsohon ɗan wasan tsakiya na Chelsea, Frank Lampard a matsayin sabon mai horar da ita.

Lampard, mai shekara 43, wanda ba shi da aiki shekara daya kenan, tun bayan da Chelsea ta sallameshi a Janairun bara, bayan wata 18 da ya horar a Stamford Bridge.

Everton ta sake ganawa da Vitor Pereira da kuma mai aikin rikon kwarya, Duncan Ferguson a karo biyu, domi zabar daya daga ciki, amma kungiyar ta sanar da nada Lampard.

An kori Rafael Benitez daga jan ragamar kungiyar, bayan da ya ci wasa daya daga 13 da ya fafata a bayannan.

Tsohon kocin Liverpool ya yi aikin ƙasa da wata bakwai, inda Everton ke mataki na 16 a kasan teburi da tazarar maki shida tsakaninta da ’yan ukun karshe.

Tun farko Everton ta yi niyyar bai wa Vitor Pereira aikin kocin, daga baya magoya baya da yawa suka taru a Goodison Park, waɗanda suka ce, ba sa bukatar Pereira a ɗauki Lampard.

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp