Everton na kokarin ci gaba da rike dan wasanta na Najeriya Alex Iwobi.
Iwobi yana cikin shekarar karshe ta kwantiraginsa da Toffees.
Dan wasan mai shekaru 26 ya kusa rattaba hannu kan tsawaita kwantaragin a farkon kakar wasan data gabata amma ya sauya ra’ayi saboda fafatawar da kungiyar ta yi.
Kungiyoyin Premier da dama sun ce suna zawarcin dan wasan mai taka leda a kungiyar amma har yanzu Everton na fatan za ta iya gamsar da shi ya kulla yarjejeniya da shi.
Merseysiders na iya tunanin siyar da Iwobi maimakon rasa dan wasan kyauta a bazara mai zuwa.
Iwobi ya buga dukkan wasanni 38 da Everton ta buga a gasar Premier a bara, inda ya zura kwallaye biyu sannan ya taimaka bakwai.
Ya koma Everton ne daga Arsenal a shekarar 2019.