Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kafa kwamitin mika mulki.
Kwamitin ya hada da wadanda aka zaba na gwamnatin El-Rufai mai barin gado da na zababben gwamnan APC mai jiran gado, Uba Sani.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta bayyana cewa, kwamitin mai mutum 65 zai shirya taswirar aiwatar da manufofin gwamnati mai jiran gado wacce ke da tushe a cikin harkokin mulki.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, kwamitin zai kuma shirya bukukuwan shigar sabuwar gwamnati.
Kwamitin mika mulki zai kasance karkashin Sakataren gwamnatin jihar Balarabe Abbas Lawal wanda shi ne shugaban kwamitin a shekarar 2015 kuma mataimakin shugaba a shekarar 2019.
Nuhu Isyaku Buzun, Babban Sakatare, Majalisar Ministoci da Harkokin Siyasa, zai kasance sakataren kwamitin, wanda nan ba da jimawa ba za a kaddamar da shi.