Bayanai sun ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na ci gaba da binciken shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta Najeriya, wato Social Investment Programme – da aka dakatar.
A jiya Talata ne jami’an hukumar suka dira a ofishin Hajiya Halima Shehu tare da gudanar da bincike, daga bisani kuma ta isa ofishin EFCC, inda suka yi mata tambayoyi har cikin dare.
Shugaba Tinubu ne ya dakatar da ita daga muƙamin babbar jami’ar hukumar NSIPA wata uku kacal bayan naɗa ta, da kuma tabbatar da ita a cikin watan Oktoba.
A baya ta taɓa aiki da ma’aikatar jin ƙai ta tarayya daga 2017 zuwa 2022.
Rahotanni sun ce shugabar ta NSIPA da aka dakatar na shirin gudanar da taron manema labarai ne a ranar Talata, lokacin da jami’ai daga hukumar EFCC suka je ofishinta a birnin Abuja.
Jaridar Punch ta ambato wata majiya na cewa an samu rashin jituwa tsakanin Halima Shehu da ministar jin ƙai ta yanzu, Dr. Betta Audu tun lokacin da ta kama aiki saboda zargin cewa ziƙau ita kaɗai tana yin amfani da kuɗaɗen hukumar waɗanda aka tanada don bayar da tallafi ga ƙungiyoyin jama’a masu rauni.
An kafa shirin ba da ƙwarewar dogaro da kai ne don tallafa wa miliyoyin ‘yan Najeriya su fita daga cikin talauci da inganta harkokin cuɗanyar al’umma da kuma samar da sana’o’i ga talakawa da ‘yan ƙasa masu rauni.
Hukumar ce kuma ke da alhakin kula da shirye-shiryen yaƙi da talauci kamar shirin ciyar da ɗalibai ‘yan makaranta na ƙasa.
An ambato Halima Shehu a baya-bayan nan yayin wani taron manema labarai a Abuja, tana jaddada ƙudurinta na tabbatar da gaskiya wajen aiwatar da shirin ba da tallafin kuɗi dala miliyan 800 na Bankin Duniya.


