fidelitybank

EFCC ta kama matashin da ya damfarar kudi Yuro 17,000

Date:

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a Benin, ta kama Irabor Kennedy Osasogie, bisa zargin zamba bayan wata kara da Antje, dan kasar Jamus ya shigar.

Matar ta kai karar hukumar cewa Osasogie, mai shekaru 21, ya damfare ta kudi Yuro 17,000.

Mai shigar da karar ta yi ikirarin cewa ta hadu da shi ta kafafen sada zumunta bayan da wani Michael Patrick ya damfare ta kudi Yuro 68,000.

Antje ta yi zargin cewa Osasogie ya nemi ya taimaka mata wajen kwato kudin amma ya ci gaba da damfarar ta Yuro 17,000.

Wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar ta ce bayan kama shi, wanda ake zargin ya ce ya samu Yuro 12,850 ne kawai.

Uwujaren ya kara da cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.”

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp