Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta kama tsohon ministan masana’antu, Charles Ugwu, kan zargin almundahanar kuɗi da ya kai naira biliyan 3.6.
An kori Mista Ugwu wanda marigayi shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua ya naɗa, bayan sauye-sauye da aka yi a gwamnati da ya shafi ministoci 19.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na EFCC Dele Oyewale ya fitar ranar Litinin, ta ce an kama tsohon ministan tare da wani Geoffrey Ekenma ne a jihar Imo ranar 11 ga watan Janairun 2024.
An bayyana cewa kama mutanen biyu na zuwa ne bayan korafi da wani bankin kasuwanci ya kai wa hukumar yana zargin wani kamfani mai suna Ebony Agro da tafka almundahana, wanda kuma yake alaƙa da tsohon ministan.
Sanarwar ta ce, “Bincike ya gano cewa an zargi Ugwuh da Ekenma da kuma Ebony Agro da karɓar rance daga bankin domin saye da dillancin shinkafar da aka gyara.


