Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi alwashin fada da duk wanda ya ce zai yi sata muddin ya zama shugaban ƙasa.
Atiku ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar masu ruwa da tsaki daga jihar Gombe da suka kai masa ziyara, karkashin jagorancin tsohon Sanata Idris Abdullahi.
Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen cin hanci a Najeriya.
“Ya isa haka, kowace ƙasa na cigaba amma ban da mu sakamakon wasu mutane kalilan da kuma rashin gwamnati na gari,” in ji Atiku.
Ya ce shugabannin haɗaka karkashin inuwar jam’iyyar ADC, za su yi aiki tukuru domin kawo canji mai nagarta wanda zai inganta rayuwar ƴan Najeriya.