Shugabannin ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya da na Turai sun gudanar da wani taro a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, domin tattauna batun rikicin Isra’ila da Gaza.
Yayin da yake jawabi a wajen taron, shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya ce babu wanda zai tilasta wa Falasɗinawa barin ƙasarsu.
“Ba za mu amince da ficewa daga ƙasarmu ba, za mu ci gaba da zama a ƙasarmu, a kowane hali kuwa”, in ji shi.
Mahmoud Abbas shi ne shugaban gwamnatin Falsɗinawa, da ke da iko da yankunan Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, to amma ba ya iko da yankin Zirin Gaza.
A baya ƙasar Masar da sauran ƙasashen Larabawa sun ce ba za a amince da kwararar Falasɗinawa domin zama ‘yan gudun hijira ba, saboda a cewarsu hakan zai tilasta fitar da su daga ƙasarsu.
Taron wanda aka yi wa laƙabi da ‘Taron Zaman Lafiya’ ya ƙunshi wakilai daga ƙasashen Jordan da Qatar da Italiya da Sifaniya da Tarayar Turai da Birtaniya.
Sai dai ba a ga wakilan ƙasashen Amurka da Isra’ila da Iran a wajen taron ba.


