fidelitybank

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Date:

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta fitar da rahoton saukar hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya, jihohi goma tare da babban birnin Tarayya, Abuja na ci gaba da fama da hauhawar farashi da ya haura kashi 30 cikin 100.

Wannan na nuna alamar cewa matsin tattalin arziki na ci gaba da gallaza wa al’umma a wasu sassan ƙasar.

Rahoton hauhawar farashi na wata-wata ya nuna cewa a watan Afrilun 2025 hauhawar farashi ya sauka zuwa kashi 23.71 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris da kuma kashi 33.69 cikin 100 a watan Afrilu na bara.

Sai dai duk da saukar farashin a matakin ƙasa, jihohin Enugu da Kebbi da Neja da Benue da Ekiti da Nassarawa da Zamfara da Delta da Gombe da Sokoto da kuma Abuja har yanzu suna fuskantar hauhawar farashi kayayyaki.

Jihar da ta fi fuskantar hauhawar farashi mafi muni ita ce Enugu inda ya kai kashi 36.0 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Na Kebbi da Niger ya kai kashi 35.1 da 34.8 cikin 100 bi da bi.

Farashin abinci na ci gaba da ƙara tsananta rayuwar jama’a a waɗannan jihohi.

A Jihar Benue, hauhawar farashin abinci ya kai kashi 51.8 cikin 100 idan aka kwatanta da bara, tare da ƙarin kashi 25.6 cikin 100 a cikin wata guda.

Wannan na da nasaba da rashin tsaro da ke kawo cikas ga noman abinci in ji rahoton.

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp