Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, ta sanar da cewa, wadanda suka yi nasara a kakar wasa ta 2023-24 za su lashe kyautar zunzurutun kudi har Naira miliyan 150.
Kyautar da ta samu a kakar wasan da ta wuce ita ce Naira miliyan 100 da Enyimba ta samu.
Shugaban NPFL, Gbenga Elegbeleye ya bayyana haka a taron kaddamar da sabuwar hukumar da aka nada.
Ya kuma bayyana cewa sabuwar kakar NPFL za ta fara ne a ranar 26 ga watan Agusta.
Enyimba ta lashe kofin NPFL karo na tara a gasar cin kofin Super Eight da aka yi a Legas a watan jiya.
Remo Stars ta zo na biyu a gasar.