fidelitybank

Direban Tireloli sun kashe hanya a Gombe sakamakon harbin abokin aikin su

Date:

Gwamnatin jihar Gombe ta yi kira da a al’ummar jihar da su kwantar da hankula, bayan wani dan sanda da ya harbe wani direban motar Tanka a lokacin da aka samu rashin jituwa a hanyar Gombe ta Dukku zuwa Darazo.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Julius Ishaya Lepes da takwaransa na ma’aikatar tsaron cikin gida da wayar da kan jama’a, Adamu Kupto Dishi ne suka yi wannan kiran yayin ganawa da manema labarai da yammacin Litinin.

Julius ya ce,”Harbin ya faru ne a lokacin da aka samu rashin jituwa lokacin da direban tankar (Abdullahi Bello) ya ki amincewa da umarnin dan sandan ga direban Tankar da ya sauko daga motarsa a shingen binciken ‘yan sanda da ke mahadar Hashidu a safiyar ranar Litinin, bayan harbe-harbe, wasu direbobin Tankar dakon man ne nan take suka tattara tankunansu tare da tare hanyar na tsawon sa’o’i da dama, domin nuna goyon bayansu ga abokin aikinsu wanda ya haifar da hatsaniya a kan babbar hanyar da ta hada Gombe da Bauchi ta hanyar Darazo da sauran jihohin Arewa maso Yamma”. Acewar su.

Ya ce, gwamnati ta sa baki cikin gaggawa, domin dakile doka da oda, saboda an kwancewa dan sandan makamai tare da kama shi, inda ya ce, a halin yanzu hukumomin ‘yan sanda a Gombe na gudanar da bincike, domin gano musabbabin faruwar lamarin.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp