Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda, ya karɓi shaidarsa ta cin zaɓen da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
A wani sako da zaɓaɓɓen gwamnan na Katsina ya wallafa a shafinsa na tuwita, ya gode wa dukkan waɗanda suka zabe shi domin mulkar jihar.
Radda ya kuma nemi taimakon ɗaukacin al’ummar jihar wajen ganin an gina kyakkyawar Katsina da kowa zai yi alfahari da ita.