Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana a matsayin wani hadadden labaran karya da aka ruwaito an yi yunkurin yin gyara ga dokar majalisar masarautun jihar da nufin dawowar tsohon sarki Muhammadu Sanusi II.
Majalisar ta kuma bayyana rade-radin cewa za su tsige sabbin sarakunan Gaya, Bichi, Rano, Karaye guda biyar domin baiwa hambararren Sarki Muhammadu Sanusi II damar samun cikakken iko a matsayin Sarkin Kano.
Kafofin sada zumunta sun yi kaca-kaca da labarin a ranar Larabar da ta gabata cewa Majalisar za ta sake duba batun masarautu, inda shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dala, zai karanta daftarin dokar 2023 a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni. 2023.
An bayyana cewa an tsara shi ne majalisar ta tattauna batun tare da amincewa da gyaran da daga baya zai bada damar tsige sarakuna da kuma dawo da Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, tare da amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba bayan kammala zaman majalisar, shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, ya bayyana labarin a matsayin labaran karya.
Hussaini ya ce babu wani yunkuri da zai sa ya karanta irin wannan gyara domin ba a taba tattauna batun ba.
‘’Abin ban dariya ne yayin da na karanta labaran karya kuma mutane da yawa suka tambaye ni ko ina sane da irin wannan shirin,’’ in ji dan majalisar.
Ya ce bayan majalisar ta amince da bukatar gwamnan na nadin masu ba shi shawara na musamman guda 20, ta dage zaman zuwa ranar Litinin 19 ga watan Yuni, 2023.
Shugaban masu rinjaye ya ce masu yada irin wadannan jita-jita mutane ne da ba sa son zaman lafiya a jihar


