fidelitybank

Dangote ya horar da ‘yan jaridu a Arewa maso Yamma

Date:

Kamfanin Dangote ya kaddamar da wani shiri na musamman na horas da ‘yan jarida sittin a Kano, a wani bangare na ayyukanta na zamantakewar al’umma.

A cewar kamfanin, horon an yi shi ne da nufin kara kaimi kan fasahar sadarwa, wanda aka zabo daga jihohin Arewa maso Yamma ciki akwai Sokoto, Katsina, Kebbi, Kano, Kaduna, Zamfara da kuma Jigawa.

Solacebase ta rawaito cewa, horon haɗin gwiwa ne tare da Folio Media and Creative Academy kuma an gudanar da shi a baya a wasu shiyyoyin ƙasar nan.

Taron na kwanaki uku mai taken: “The Convergence Journalism”.

A taron wanda aka fara gudanar da shi jihar a Kano ranar Laraba, wanda babban Jami’in Kamfanin, Branding and Communication, Anthony Chiejina, ya ce an shirya horaswar ne, domin inganta kwazon ‘yan jarida kan dabarun yada labarai.

Ya ce” horon zai taimaka wajen samar wa manema labarai damar tunkarar kalubalen da ke tattare da su musamman ma, sabbin kafafen yada labarai tare da bayyana kafafen yada labarai a matsayin abokan hadin gwiwa da ake samu. Inji Anthony.

Mai gudanar da yyyukan na Folio Media and Creative Academy, Alabi Pius, ya ce, “(FMCA) ita ce ta horar da Folio Communications Plc. Mawallafin jaridar Daily Times, kuma wannan horon zai baiwa ‘yan jarida da shugabannin kafafen yada labarai da jami’an hulda da jama’a da sauran kwararru a aikin”.

latest nigeria newstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp