‘Yan takarar gwamna na jam’iyyar Labour a jihar Jigawa, Tsoho Garba da dukkan ‘yan takarar majalisar wakilai ta kasa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Tsoho Garba ya tabbatar da haka a ranar Asabar bayan ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Dutse babban birnin jihar.
Sai dai ya ce, shugaban jam’iyyar LP na jihar da kusan dukkanin shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 27 na jihar sun koma jam’iyyar APC.
Tsoho ya ce sun yanke shawarar janye takararsu da jam’iyyarsu ta APC ne domin nuna godiya ga gagarumin ci gaban da Gwamna Badaru Abubakar ya yi a jihar.
“Mutane sun bukaci mu tsaya takara a karkashin jam’iyyar Labour, amma a ziyarar yakin neman zaben da muka yi a fadin jihar duk mun san yadda gwamnatin APC ta sauya jihar ta hanyar ayyuka da shirye-shirye masu tasiri kai tsaye ga talaka”.
“Idan har muna takara ne domin neman ci gaban jiharmu, babu shakka abin da Jigawa ke bukata shi ne a ci gaba da zama, kuma abin da ya fi dacewa shi ne a bar APC ta ci gaba da jan ragamar mulki domin kada ta kauce daga babbar hanyar. ”
“Don haka daga yau dukkanmu da abokan siyasarmu mun koma APC kuma mun sha alwashin yin aiki domin samun nasarar ta a matakin kasa da jiha a babban zabe mai zuwa”.
Da yake karbar wadanda suka sauya sheka, Gwamna Badaru Abubakar ya yaba da kudurinsu na ci gaban jihar tare da yi musu alkawarin ba su duk wani hakki da tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar suka samu.