Shugabar Kotun Daukaka Kara a Najeriya, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ba da umarnin a mayar da duk kararrakin da aka daukaka na shari’o’in zaben watan Fabrairu da na Maris zuwa Abuja da Legas.
Tashar talbijin ta Channels TV ta ruwaito cewa umarnin ya shafi dukkan kararrakin da aka daukaka na zaben gwamnoni, da na ‘yan majalisar tarayya, da kuma na jihohi.
Tashar ta ce kararrakin da aka daukaka daga kotunan sauraron zabe a jihohi, kamata ya yi a saurare su a kotunan daukaka kara 20 da ke fadin kasar, amma yanzu rassan kotun biyu ne kacal za su yi alkalanci a kansu.
Channels ta ambato majiyoyi a Kotun Daukaka Karar na cewa reshen kotun na Abuja ne zai saurari kararrakin zaben da aka daukaka daga jihohi 19, yayin da kararrakin zabe na jihohin kudu 17 za a saurare su a Legas.
Ta ce an ba da umarnin ne bayan zarge-zarge da korafe-korafen da aka shigar a kan alkalan kotunan jihohi.
Wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu sun yi zargin cewa wasu sun sanya alkalan kotunan zabe karya ka’idar aiki.
Ta ce jam’iyyun da suka fusata sun kuma nuna damuwar cewa irin haka ce mai yiwuwa za ta faru idan aka saurari kararrakin da aka daukaka a jihohi.
Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem kamar yadda Channels ta ruwaito, na cewa mayar da shari’o’i zuwa sassan kotun kalilan zai ba ta damar sanya ido a kan alkalan yadda ya kamata.


