fidelitybank

Dalilin da ya sa na bar Chelsea zuwa Manchester United – Mount

Date:

Mason Mount ya ce gamsuwar da ya yi da bayanin kocin Manchester Erik Ten Hag na yadda zai yi amfani da shi ce ta sa ya bar ƙungiyar da ya taso a cikinta.

Ɗan shekara 24 shi ne na farko da Ten Hag ya ɗauka a bana, a cinikin da aka yi na fan miliyan 55, da ƙarin miliyan biyar na wasu tsarabe-tsarabe.

Mount ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar ne da kuma zaɓin ƙara shekara guda idan ta ƙare.

“Bayan haɗuwa da kocin ƙungiyar ya yi min bayanin shirinsa a ƙaina, sai na ji kamar a fara kakar ta bana yanzu,” in ji ɗan wasan Ingilan.

“Ko wa zai zama shaida cewa ƙungiyar ta haɓɓaka ƙarƙashin mai horaswa Erik ten Hag.

“Ina da matuƙar buri, Na san daɗin da ake ji idan an lashe manyan kofuna kuma nasan aikin da ake yi ba dare ba rana. Zan yi komai da ƙarfin iyawata a Manchester United.”

Sau uku Chelsea na ƙin amincewa da tayin da United ta yi kan Mount kafin daga baya ta amince.

A bara ƙungiyar ta Landan ta kashe fan miliyan 600 wajen sayan ‘yan wasa, amma yanzu dole ta sayar da wasu domin samun sauƙi game da dokar taƙaita kashe kuɗi.

Chelsea ba ta so rabuwa da ɗan wasan da ta raina ba tun yana shekara shida, amma ta gaza cimma matsaya wajen sabunta kwantaraginsa da za ta ƙare a baɗi.

“Ba abu ba ne mai sauƙi barin kulob ɗin da ka taso a cikinsa, amma tafiya Manchester zai sake buɗe wani sabon babin ƙalubale a rayuwata,” in ji Mount.

“Ganin na buga wasa da su a baya, na san ƙarfin da ƙungiyar take da shi, zan so zama cikin waɗanda za su riƙa cin manyan kofuna ko da yaushe.”

Monut wanda ya ci wa Chelsea kwallo 33 cikin wasa 195 da ya buga wa Chelsea tun bayan zamansa babban ɗan kwallo a 2019, bai samu buga wasu wasanni ba a ƙarshen kakar da ta gabata saboda rauni da ya ji, wanda Blue suka ƙare a na 12, rashin ƙoƙari da suka yi kenan na farko cikin shekara 25.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp