Mawaki, Oladapo Oyebanji, Dbanj ya bayyana dalilin da ya sa hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta sake shi daga tsarewar da ta yi masa.
Ku tuna cewa an tsare Dbanj ranar Laraba bisa zargin hada baki da wasu ‘yan siyasa da bankuna domin karkatar da kudaden N-power.
Mawakin dai ta bakin lauyansa ya ce ba shi da wata alaka ta kwangila ko wata alaka da wata kungiya ko mutane a ciki ko wajen Gwamnati.
Ya kuma kalubalanci ICPC da ta bayyana sunayen jami’ai da ‘yan siyasa, wadanda ke da hannu a cikin yarjejeniyar.
Sai dai an sake Dbanj a ranar Juma’a, bayan shafe kwanaki uku a tsare.
Da yake rubutawa a shafinsa na Instagram, Dbanj ya ce, an sake shi ne bisa son ransa saboda ICPC ba ta samu komai a kansa ba.
Ya kuma godewa ‘yan Najeriya tare da bayyana kwarin gwiwar cewa ICPC za ta bankado gaskiya.