fidelitybank

Dalilin da ya sa a ka aiyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda — Osinbajo

Date:

 

 

 

 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta aiyana ‘yan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda a hukumance shi ne don baiwa jami’an tsaro damar ɗaukar tsauraran matakai a kansu.

Mataimakin shugaban ƙasan ya baiyana haka ne a fadar Sarkin Katsina a ranar Asabar domin yin ta’aziyya ga Dahiru Barau Mangal, wanda ya rasa mahaifiyarsa, Hajiya Murja.

Osinbajo ya kuma baiyana fatansa na cewa dukkan sabbin matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta sun sanya ya kamata a iya ganin sauyi mai ma’ana sosai a harkar tsaron Nijeriya.

Yayin da yake mika godiyarsa ga Sarkin Katsina da sarakunan sa bisa kyakkyawar tarba da aka yi masa, Osinbajo ya yi addu’ar Allah ya ba wa masarautarsa ​​da ƙasa baki daya zaman lafiya.

Ya baiyana ƙwarin gwiwa ce za a samu wadata da farin ciki da kuma zaman lafiya a ƙasar nan kafin wa’adin mulkinsu ya ƙare.

Da yake mayar da martani, Sarkin Katsina, ya bayyana farin cikinsa da ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a hukumance.

 

the nation news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamna Zulum ya musanta shirin sauya sheƙa zuwa ADC

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya musanta...

Tinubu ta ceci Najeriya faɗa wa cikin mawuyacin hali – Ribadu

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam...

Isra’ila za ta aika tawaga Qatar don tattaunawa da Hamas

Isra’ila ta yanke shawarar aika wata tawaga zuwa Qatar...

Jagoran Iran ya bayyana gaban jama’a karon farko tun soma yaƙi da Isra’ila

Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana...

Muna aiki tukuru don bunƙasa noma a Najeriya – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya tabbatar da cewa...

Duk wanda ya yi sata idan na zama shugaban ƙasa sai na yake shi – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi alwashin...

Ina nan a PDP na ban gudu ba – Adeleke

Gwamnan jihar Osun, ya musanta rahotonnin da ke cewa...

Tinubu ya isa birnin Rio na Brazil don halartar taron BRICS

Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Rio de...

Matakan da muke ɗauka kan kisan matafiya a Plateau – Mutfwang

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, ya ce gwamnatinsa...

Tinubu ya gaji tattalin arziki da ya kusa durkushewa – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyeson Wike, ya ce...

Har yanzu PDP tana nan da ƙarfinta – Isa Ashiru

Yayin da fagen siyasar Najeriya ke ci gaba da...

An kama ɗan shekara 70 kan zargin kashe ƙanwarsa a Jigawa

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta...
X whatsapp