Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilan da suka sa ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakinsa a zaben 2023 mai zuwa.
Da yake jawabi a shelikwatar PDP ta kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, Atiku ya shaida wa taron da ya kunshi shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, cewa ya kai ga yanke shawarar zabar Okowa a matsayin mataimakinsa bayan ya yi shawarwari da gwamnonin jihohi. a dandalin jam’iyyar, kwamitin ayyuka na kasa, kwamitin amintattu da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce, “Na bayyana a fili cewa abokin takarara zai samu damar ya gaje ni a nan gaba kadan, wato shugaban kasa mai jiran gado.
Wato dole ne mutum ya kasance yana da halayen da zai zama Shugaban kasa. Dole ne mutun ya san irin rugujewar da gwamnatin APC ta jefa kasarmu a ciki.
Dole ne ya fahimci irin wahalhalun da akasarin al’ummarmu suke ciki da gaggawar kawar da su daga wannan wahalhalu, ya fahimci muhimmancin bunkasar tattalin arziki da ci gaba don samar wa matasanmu ayyukan yi, da fata, da hanyar samun arziki.