Alamu na nuna cewa gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya zama allurar cikin ruwa, wanda ‘yan Magana kan ce mai rabo ka dauka sakamakon yadda ‘yan takarar shugaban kasa na manyan jam`iyyun siyasar Najeriya ke ribibin jan sa a jika.
Ko a makon da ya wuce ɗan takaran jam`iyyar APC Bola Tinubu da na Labour, Peter Obi da kuma na PDP Atiku Abubakar sun gana da Wiken a London.
Wasu makwannin da suka wuce ma ɗan takaran shugaban kasa na jam`iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai masa irin wannan ziyarar zawarcin.
Ko me ya sa ake wannan kokuwar a kan sa? Dr Abubukar Kari masanin siyasa ne a jami`ar Abuja, kuma ya shaidawa BBC cewa gwamna ne na wata jiha mai dimbin jama’a da ke kusan mataki na 7 a yawan masu kaɗa kuri’a.
Sannan a sashin kudu maso kudancin Najeriya babu hamshaƙin ɗan siyasa irinsa, sannan ya na da karfin faɗa a ji tsakanin wasu hamshaƙan ‘yan siyasa a jihohi da masu arziki.
Wannan na daga cikin dalilin da ya sa ‘yan siyasa ke ganin idan suka yi zawarcinsa zai ba su tagomashi a takararsu.
Sai dai masanin na cewa da wuya ya iya barin PDP, ganin cewa ya gina kasan a jam’iyyar, sannan yana da manyan yara da ya gina yanzu haka suke takara.
Babu shaka a cewar masanin Wike na iya yiwa jam’iyyar PDP zagon-kasa, wannan shi ne dalilin da ya sa ake zawarcinsa, sannan ɗan takarar shugabanci kasa na PDPn Atiku Abubakar ke son sulhu da shi.
Masanin ya ce babu taƙamaimai abin da za a iya cewa ga shi abin da yake so, sai dai yana son ƙara karfinsa ne na faɗa aji.
Amma a cewar masanan idan mulki ya fita daga hannunsu karfin faɗa ajinsa zai ragu, dalilin da ya sa ya ke son sake gina tagomashinsa kenan kafin zaɓen 2023.


