Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a yau 24 ga Mayu, 2022, sun kai farmaki gidan Sanata Rochas Okorocha, Maitama, Abuja, domin kama shi.
Matakin, a cewar kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya biyo bayan kin amsa gayyatar da tsohon gwamnan Imo ya yi ne.
Uwujaren ya ce, Okorocha ya tsallake belin gudanarwa da Hukumar ta ba shi tun da farko.
An mika karar ga mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Amma sau biyu yunkurin gurfanar da Sanata Okorocha ya ci tura, saboda rashin halartar tsohon gwamnan da ya kaucewa gudanar da ayyuka.
A ranar karshe da aka dage zaman, 28 ga Maris, 2022, Mai shari’a Ekwo kafin ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 30 ga Mayu, 2022, ya yi gargadin cewa “dage shari’ar ne na karshe da zan bayar kan wannan batu.