fidelitybank

Daga yanzu babu wanda zai sake raina mai zaɓe a Najeriya – Buhari

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce, zaɓukan 2023 sun nuna yadda mulkin dimokuraɗiyya ke ci gaba da ginuwa da kuma samun karfi musamman ma ta yadda masu zaɓe suka waye da kuma sanin shugabannin da za su zaɓa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin sabon Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hamim Nuhu a fadarsa da ke Abuja, inda ya ce, sakamakon zaɓen gwamnoni guda 10 da suka kasa samun nasarar zuwa majalisar dattawa, ya nuna cewa yanzu babu tabbas game da samun mulki kuma yanzu masu zaɓe su ke da wuƙa da nama.

Karanta Wannan: Ɗan takarar mu Obi ake hari ba jam’iyyar mu ba – LP

“Hakan ya nuna cewa, dimokuraɗiyyar mu na ƙara girma da kuma yadda masu zaɓe suka waye. Abin da ya bani mamaki shi ne ɗan Najeriyar da aka raina, a yanzu shi ke da wuƙa da nama wajen zaɓar wanda ya dace,” in ji Buhari.

“An mayar da cewa bayan gwamna ya yi shekara takwas, daga nan zai tafi majalisar dattawa ba tare da shan wahala ba. Daga yanzu babu wanda zai sake raina mai zaɓe a Najeriya. Siyasa za ta zama abu mafi wahala nan gaba,” a cewar Buhari.

Da yake magana, sabon Sarkin na Dutse, Alhaji Muhamamd Hamim, ya gode wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari saboda taimaka wa jihar Jigawa ta samu ci gaba a ɓangaren noman shinkafa da amincewa da gina layin dogo daga Kano zuwa Dutse da kuma dawo da zaman lafiya a jihar

vanguardnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...
X whatsapp