Gwamnatin jihar Edo, za ta fara daukar ‘yan sandan dazuzzuka, biyo bayan tantancewa da dazuzzukan jihar ya yi.
Crusoe Osagie, mai ba Gwamna Godwin Obaseki shawara na musamman kan harkokin yada labarai, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin 1 ga watan Agusta, ya ce, daukar ma’aikatan wani bangare ne na wani sabon yunkurin inganta tsaro a fadin jihar.
Osagie ya ce, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki na karfaf tsarin tsaro tare da daukar matakai daban-daban na tabbatar da tsaro a jihar, da suka hada da tsefe daji, rajistar babura da kasuwanni, sanya hannu kan dokar hana kiwo, da rajistar mazauna jihar, daga cikin wasu.
Sanarwar ta ce; “Hakin kowace gwamnati a kowace al’umma shi ne tabbatar da tsaro da tsaron jama’a. Babu wata gwamnati da za ta iya kiran kanta a matsayin gwamnati idan ba za ta iya kare rayukan al’ummar da take sa ido ba da kuma tabbatar da rayuwarsu.
“Don haka ne mu a Edo, duba da abin da ke faruwa a kasar nan a yau, mun yanke shawarar cewa, tsaro a yanzu shi ne babban fifikonmu. A bangaren dazuzzukan mu, mun kammala tantancewa da tantance duk dazuzzukanmu na Jihar Edo, musamman a Edo ta Kudu.


