Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun yi garkuwa da wasu mutanen kauyen Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara da ba a tantance adadinsu ba.
THEWILL ta ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne a ranar Alhamis inda suka yi garkuwa da mutanen kauyen da dama.
Wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 10 na dare, inda suka fara harbe-harbe a sama.
Ya lura cewa ‘yan bindigar ba su kashe kowa ba, saboda a fili suna so su sace mutanen kauyen.
“Duk da cewa ba su kashe kowa ba, sun yi awon gaba da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a yayin aikin. Kwanaki uku da suka wuce, sun kashe mutum daya tare da satar shanu,” inji shi.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba ta mayar da martani kan lamarin ba, har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sanar da kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a rikicin kananan hukumomin Guyuk da Lamurde da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane.
Rundunar a kokarinta na ganin ta kawo karshen rikicin da ya barke a unguwannin kananan hukumomin, ta kama mutane kusan shida da ake zargi da hannu a rikicin.